Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ma’aikatan kungiyar tsaro ta IPOB ne, sun kashe Hausawa ‘yan kasuwa hudu a jihar Imo.
Wani Bahaushe a jihar ya shaida wa manema labarai cewa an kashe ’yan Arewa uku a Orlu yayin da aka kai hari kan mutum na hudu a karamar Hukumar Umuaka Njaba.
An kuma yi jana’izar wadanda aka kashe kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.