fbpx
Thursday, May 6
Shadow

Wasu ‘yan Bindiga sun kashe wani mutum a gaban Iyalansa

An bayyana cewa an harbe Ehiorobo a gaban matarsa mai ciki da kuma yaransa a cikin gidansa da ke kan titin Peanut da ke kan hanyar Sapele a cikin garin na Benin da misalin karfe 2 na dare a ranar Alhamis, 18 ga watan Fabrairu.

Ance yan bindigar sun ketara gini sannan suka samu damar shiga cikin gidan ta hanyar balle kofa.
Da shigar su, kai tsaye suka shiga cikin ɗakin kwanan shi, suka jawo shi zuwa falo kafin su harbe shi a kai.

An ce Ehiorobo ya roke su da su kyale shi kuma zai basu duk abunda suke so, amma suka ce masa sun zo ne kawai domin su kashe sa.

Matar mamacin da ke dauke da juna biyu ta fada wa manema labarai cewa an kashe mijinta a gabanta da ’ya’yansu.

Matar cikin kuka, ta kara da cewa duk da mijinta ya roke su da su kyale shi, sai da suka harbe sa kuma suka tabbatar ya mutu kafin subar gidan.

Yan sanda sun kwashe gawar zuwa dakin ijiye gawarwaki domin gudanar da bincike na musamman.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *