fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Wasu kwararrun mafarauta sun cafke mutum biyar masu garkuwa da mutane a jihar Kogi

Wasu kwararrun mafarauta a karamar hukumar Okehi da ke jihar Kogi sun cafke mutum biyar daga cikin fitattun masu garkuwa da mutane.

An cafke mutanen biyar da ake zargi da safiyar ranar Asabar a Atami, wani yanki na yankin Osara a ranar Talata, 27 ga watan Satumba.

Babban mataimaki ga shugaban karamar hukumar Okehi, Hon Abdulraheem Ohiare Ozovehe a kan Kafafen Yada Labarai, Sarki Habib, wanda ya tabbatar da kamun a cikin wata sanarwa, ya ce kungiyar ta dade tana addabar hanyar Okene zuwa Lokoja da hanyar Okene zuwa Auchi na jihar Kogi.

Sanarwar ta ce a halin yanzu wadanda ake zargin suna tare da hukumomin tsaro yayin da ake ci gaba da bincike don kwato manyan makamansu.

Wadanda ake zargin sune: Tukur Saleh, Ahmadu Sanni, Yusuf Sanni, duk daga Bauchi; Abubakar Saleh (Baba Wuro) da Isah Saleh, duk daga jihar Kano.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *