fbpx
Friday, May 14
Shadow

Wasu mutane 6 sun tsallake rijiya da baya a wani hatsarin mota da ya faru a Jihar Osun

Mutane shida sun tsallake rijiya da baya yayin da wasu motoci biyu suka yi karo a kan titin Dada Estate a Osogbo, jihar Osun.

Hatsarin ya faru ne a safiyar Juma’a, 30 ga Afrilu, a cewar hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC).

Kakakin hukumar FRSC a jihar, Misis Agnes Ogungbemi, a cikin wata sanarwa ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 12.45 na safe.

Ogungbemi ta bayyana cewa fasinjojin shidda sun ketare rijiya da baya a lokacin da wata mota kirar Toyota Camry mai lamba AAB53AJ ta yi karo da karamar motar Suzuki (Korepo) mai lamba SGB914XA.

A cewar ta, an kai mutanen biyu da suka jikkata zuwa asibitin koyarwa na Ladoke Akintola (LAUTECH) don kula da lafiyarsu.

Ogungbemi ta kuma yi kira ga masu ababen hawa da sauran masu amfani da hanyar da su bi dokokin hanya kuma su guji duk wani abin da zai haifar da asarar rayuka da dukiyoyi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *