fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe wani Manjo Janar a kan hanyar Lokoja zuwa Abuja

Wasu ‘yan bindiga sun kashe Manjo Janar Hassan Ahmed, tsohon Provost Marshal na Sojojin Najeriya.

Wata sanarwa da rundunar sojan Najeriya ta saki a safiyar yau ta ce an kashe Ahmed ne a kan hanyar Lokoja zuwa Abuja a ranar Alhamis, 15 ga watan Yuli.

Majiyoyin dangi sun ce yana dawowa daga Okene lokacin da ‘yan bindigar suka bude wuta kan motarsa.

Wata sanarwa da kakakin rundunar, Onyema Nwachukwu ya fitar, ta ce za a binne mamacin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a yau 16 ga watan Yuli.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *