fbpx
Thursday, May 6
Shadow

Wasu ‘yan bindiga da suka nuna kansu a matsayin yan bikin jana’iza sun kashe‘ yan sanda 3 a shingen binciken ababan hawa

Wasu ‘yan bindiga sun harbe‘ yan sanda uku har lahira a jihar Ebonyi.

Yan sandan uku suna bakin aiki ne a kan babbar hanyar Ogoja-Abakaliki a matsayin wani bangare na tawagar ‘yan sintiri na Safer Highway lokacin da aka kai musu hari a ranar Laraba.

Kakakin rundunar ‘yan sanda Loveth Odah ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce maharan sun yi kama da wadanda za su je bikin jana’iza.

DSP Odah ya ce maharan sun jero akan ababen hawa; babura uku a gaba, a bayan kuma babura masu kafa uku, suma guda uku yayin da motocin Sienna biyu suka bi su a baya.

Ta ce, “Lokacin da suka isa shingen binciken‘ yan sanda, sai aka tsayar da su don bincike, nan take; suka bude wuta kan jami’an ‘yan sanda, inda suka kashe biyu da ke kusa da wurin.

Ta kuma ce mutanen da ke cikin Babur mai kafa uku a yayin da suka isa inda motar‘ yan sanda ta tsaya tare da wani dan sanda guda a wurin binciken ababen hawa, suka harbe dan sandan kuma suka cinnawa motar ‘yan sandan wuta. Hakan ya sa suka zama ‘yan sanda uku suka rasa a jiya”.

Ta ce an tura tawagar ‘yan sanda karkashin jagorancin Mataimakin Kwamishina a zuwa yankin domin cikakken bincike akan abin da ya faru.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *