fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

Wasu yan bindinga da ake zargin makiyaya ne sun sace manomi da ya’yansa hudu a Jihar Oyo

Wasu yan bindinga da ake zargin makiyaya ne sun sace wani manomi mai suna Rasaq Jamiu, da ’ya’yansa hudu a kauyen Maami da ke karamar Hukumar Ibaraoa ta Arewa a Jihar Oyo.

A cewar rahotanni, Jamiu ya tafi gonar sa dake a kauyen Maami a ranar Litinin, 19 ga Afrilu lokacin da masu garkuwar suka afka cikin gonar, suka sace shi tare da ya’yansa.

Daga baya ‘yan bindigar sun saki ya’yansa amma shi Jamiu an yi garkuwa da shi kuma wadanda suka sace shi suna neman kudin fansa Naira miliyan 5 kafin su sake shi.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Sakataren kungiyar manoma a Ibarapaland, Taiwo Adeagbo, wanda aka fi sani da Akowe Agbe, ya ce an sace Jamiu da misalin karfe 12 na ranar Litinin.

Har yanzu rundunar ‘yan sanda ta jihar ba ta ce komai game da wannan ci gaban ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *