fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Wata babbar Kotu ta daure wasu mutane 3 bisa laifin satar batirin mota a Abuja

Wata babbar kotun yankin da ke Zuba Abuja, a ranar Alhamis ta ba da umurnin cewa a tsare wasu leburori uku, wadanda suka amsa laifin satar batirin mota a cibiyar gyara.

Rundunar ‘yan sandan ta gurfanar da wadanda ake zargi guda uku, wadanda aka bayyana sunayensu da Isaac Musa, Bulus Musa, da Amos Audu, wadanda dukkansu ke zaune a kauyen Angwan Saywa, Abuja, da hadin baki, wuce gona da iri da sata.

Alkalin kotun, mai shari’a Gambo Garba, ya bayar da umurnin a ci gaba da tsare su a cibiyar kula da gyara hali ta Najeriya da ke Suleja a jihar Neja har zuwa ranar 8 ga watan Satumba domin yanke musu hukunci.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *