fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

Wata cuta mai rikitarwa ta kashe mutane 59 a China

Mutane 59 sun rasa rayukansu sakamakon wata cuta mai rikitarwa da aka gaza shawo kanta a China.

Mahukuntan lafiya na kasar sun bayyana cewar a garin Vuhan an samu mutane da dama da suka kamu da cutar mai janyo wahalar yin numfashi inda kuma ba ta yi kama da cutar MERS da murar tsuntsaye da aka saba gani a kasar da Gabas ta Tsakiya ba.
Mahukuntan Hong Kong kuma sun ce cutar Nimoniya ce, kuma a kwanakin da suka gabata ta kama mutane 15.
Alkaluman Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya WHO na cewa ya zuwa yau a duniya baki daya mutane sama da dubu 8 ne cutar MERS ta kama inda 775 daga cikinsu suka mutu.
Sakamakon bullar cutar ta MERS a shekarar 2003 mutane 349 a China da 299 a Hong Kong ne suka mutu.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *