fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Wata da akawa Auren dole a Adamawa ta kashe mijinta

Wata matashiya da akawa auren dole a Adamawa ta kashe mijinnata.

 

Rumasa’u Muhammad me shekaru 19 daga kauyen Wuro Yanka na karamar hukumar Shelleng ta kashe mijinta me shekaru 35.

 

Kakakin ‘yansandan jihar, Suleiman Nguroje ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace iyayen yarinyar sun mata auren dolene.

 

Ya kuma kara da cewa, kwamishinan ‘yansandan jihar yace a yi cikakken bincike dan hukunta me laifin.

 

Saidai ya jawo hankalin iyaye su dainawa ‘ya’yansu auren dole.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *