fbpx
Monday, October 25
Shadow

Wata daya da sace sarkin Bungudu har yanzu ba labari

Al’ummar masarautar Bungudu a jihar Zamfara na ci gaba da jimami da jiran tsammani da rashin tabbas kan makomar Sarkin Bungudu Alhaji Hassan Attahiru da ƴan bindiga suka sace.

Kusan wata ɗaya kenan babu labarin Sarkin mai daraja ta ɗaya a jihar Zamfara wanda aka sace kan hanyarsa ta zuwa Abuja daga Kaduna.

Akwai ɗan sanda ɗaya da aka kashe lokacin da ƴan bindigar suka yi awon gaba da sarkin a ranar 14 ga watan Satumban da ya gabata.

A ziyarar da BBC ta kai fadar sarkin Bungudu, mutanen masarautar sun ce har yanzu babu wani labari game da Sarkin nasu.

Sakataren masarautar Bungudu, Alhaiji Usman Ibrahim ya ce suna cikin hali na kaɗuwa yadda babu wani labarin sarkin.

Ya faɗawa BBC cewa tun bayan faruwar lamarin ba su da cikakken bayani kan halin da Sarkin yake ciki, musamman ma saboda rashin sadarwa a wasu yankunan jihar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *