fbpx
Monday, September 27
Shadow

Wata kotu ta bai wani mutum damar ya saki matarsa ​​wadda ya zargin ta da yin madigo

Kotu ta ba wani mutum damar ya saki matarsa da ya hadu da ita a Facebook saboda kasancewarta ‘yar madigo

 

Wata kotu a kasar Kenya ta bai wani mutum damar ya saki matarsa ​​wadda ya zarge ta da yin madigo.

Mutumin mai shekaru 30 ya shaidawa kotu a gundumar Nakuru cewa ya sadu da matarsa ​​a Facebook a 2015 kuma sun yi aure shekara.

Ya shaida wa kotun cewa ya sha wahala a hannun matarsa ​​yayin da ta hana shi haƙƙinsa na aure.

A cikin takardun kotu, mutumin ya ce tsawon watanni takwas bayan aurensu, matarsa ​​da ta rabu da shi ta hana shi haƙƙoƙin aure. A cewar takardun kotun, mutumin ya gano cewa matarsa yar madigo ce ta hanyar kanwarsa domin tana nuna wasu hallaya na sha’awa idan taga kanwarsa.

Babban alkalin kotun Nakuru, Yvonne Khatambi wanda ya yanke hukunci kan lamarin ya ce tuni auren ya rabu saboda dukkan bangarorin biyu sun kasa yin sulhu a tsakanin su.

Khatambi ya ce;

“Bangarorin da aka bayyana a matsayin FJO da PNM sun kasa yin sulhu duk da kokarin ganin an daidai ta su.

“Da haka na raba auren tsakanin mai karar da wanda ake kara.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *