fbpx
Saturday, June 19
Shadow

Wata Marainiya ta yi barazanar kashe kanta idan ba’a kai mata dauki kan lalata da ita da kawunta yake ba

Wata matashiya da ba’a bayyana sunanta ba, ta rubuta takarda ta ajiye a gidan makwautansu inda tace zata kashe kanta.

 

Matashiyar marainiyace wadda bayan rasuwar mahaifinta sai ta koma zama da kawunta, Peter Ezeka.

 

Yarinyar ta samu daukin makwauciyarsu, Rita, wadda ta kaiwa ‘yansanda rahoton faruwar lamarin, tace tun tana da shekaru 10 ne a shekarar 2017 take zaune da kawun nata.

 

Ta kara da cewa kuma matar kawun nata tasan yana mata fyade inda har ta nemo Fasto yayi addu’ar cewa, idan ta fada zata haukace.

 

Saidai mahaifiyar yarinyar ta bayyana cewa a saki Peter saboda run bayan da mijinta ya rasu, yake taimakonta kuma gashi yana rike da diyarta. Tace kuskurene abinda yawa diyartata. Saidai ana zargin ya bata kudi ne, kamar yanda FIJ ta ruwaito.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *