fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

Wata mata mai shekaru 20 ta sha snipper don kashe kanta bayan mijinta ya saketa a jihar Jigawa

Wata mata ‘yar shekara 20, Dausiyya Dahiru ta yi yunkurin kashe kanta bayan mijinta ya sake ta a jihar Jigawa.

Lamarin ya faru ne da yammacin Litinin a garin Roni, karamar hukumar Roni ta jihar Jigawa.

Bincike ya nuna cewa matar ta sayi maganin kwari kuma ta yi amfani da shi a cikin abincin ta bayan ta gaza a yunkurin ta na hana mijinta auren mata ta biyu.

Matar da mijinta sun samu sabani bayan da ya bayyana shirinsa na auran matar ta biyu.

Kakakin ‘yan sanda, ASP. Lawan Shiisu Adam ya tabbatarwa da faruwar lamarin.

Ya ce ‘yan sanda da ke yankin sun samu labarin cewa matar ta yanke shawarar kashe kanta ne saboda mijinta ya sake ta.

Shiisu ya ce yarinyar ta suma nan da nan bayan ta sha maganin sannan aka garzaya da ita asibiti a Roni don kula da lafiyarta.

Ya ce matar tana amsar magani, yayin da lamarin ke ci gaba da bincike.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *