fbpx
Monday, November 29
Shadow

Wata mata tayi garkuwa da kanta domin karbar N50,000 daga mijinta

Rundunar ‘yan sandan jihar Ekiti ta kama wata matar aure, Sule Nana, bisa laifin yin garkuwa da kanta da nufin karbar kudi naira 50,000 daga hannun mijinta.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Sunday Abutu wanda ya gabatar da ita tare da wasu wadanda ake zargi a ranar Laraba a Ado-Ekiti, babban birnin jihar, ya ce mutanen Rapid Respond Squad ne suka kama wadda ake zargin bayan gudanar da bincike mai zurfi.

A cewar PPRO, jami’an RRS a ranar 20 ga Nuwamba, 2021, sun samu kiran waya daga Nana cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi garkuwa da ita a hanyar Ifaki-Oye-Ekiti.

Da take magana, wadda ake zargin ta ce ta yanke shawarar yin garkuwa da kanta ne domin ta samu kudi daga wajen mijinta da ‘yan uwanta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *