fbpx
Saturday, June 19
Shadow

Wataran fa zamu tashi mu ga Boko Haram ta kafa tuta a Aso rock>>Pat Utomi

Shahararren masanin tattalin arziki, Farfesa Pat Utomi ya bayyana cewa, matsalar tsaron Najeriya ta yi yawa.

 

Yace matsalar ta rika karuwa a hankali yayin da muka rika yaudarar junan mu da cewa zata yi sauki nan gaba, har abu gashi yanzu ya zama yanda ya zama.

 

Yace mutane na rayuwa da fargabar me zai iya faruwa anjima, wanda hakan daidai yake da ace mutum ya mutu. Ya kuma kara da cewa, kudin kayan abinci na ta hauhawa kasancewar manoma basa iya zuwa gona.

 

Yace nan gaba idan ba’a yi hankali ba, za’a tashi a ga Boko Haram sun kafa tuta a Fadar Shugaban kasa ta Aso Rock.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *