fbpx
Sunday, September 26
Shadow

WhatsApp ya ɓullo da sabon tsarin ɓacewar hotuna da bidiyo

Manhajar WhatsApp ya ɓullo da sabon tsarin da zai bai wa masu amfani da shafin damar ɓatar da hotuna da bidiyon da aka aiko musu bayan dan wani lokaci.

Bayan wanda aka aikawa hoton ko bidiyon ya bude su a karon farko, za su ”kalla sau daya”, daga nan sai ya goge da kan shi ba tare da ya fada ma’ajiyar hotuna da ke cikin wayarsa ba.

WhatsApp ya ce an dauki matakin ne domin bai wa masu amfani da shi karin damar sarrafa shi yadda suke bukata, da samun karin kariya.

Sai dai, masu kare hakkin yara su na nuna damuwa kan bacewar hotunan ko sakwannin ko da kuwa mutum bai bukaci hakan ba, zai taimaka kan boye wata shaida musamman idan an ci zarafin yara ta hanyar lalata.

Dama dai ana takun saka tsakanin hukumar yaki da cin zarafin kananan yara ta kasa da kasa da uwar manhajar WhatsApp, wato Facebook kan amfani da sakon sirri.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *