fbpx
Wednesday, January 26
Shadow

Ya kamata awa Nnamdi Kanu Afuwa>>Ohanaeze Indigbo

Kungiyar kare muradun inyamurai ta Ohanaeze Indigbo ta bayyana cewa, kamata yayi awa shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu Afuwa.

 

Kungiyar ta bayyana hakane inda tace akwai irin Nnamdi Kanu din da yawa da aka musu afuwa.

 

Gwamnatin tarayya na zargin Nnamdi Kanu da cin amanar kasa da kuma juyawa gwamnati baya.

 

Shugaban kungiyar Ohanaeze Indigbo, Eorge Obiozor ya bayyana cewa, hanya daya da za’a magance matsalar shine a bi ta lalama.

 

Saidai a hira ta karshe da aka yi da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, ba zai iya sakin Nnamdi Kanu ba saboda ba zaiwa bangaren shari’a katsalandan ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *