fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

Ya kamata CBN ta biya Diyyar Miliyan 100 da ‘yan Bindigar da suka sace daliban Kaduna suka nema kamin Lokaci ya kure>>Sheikh Gumi

Babban Malamin Addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi ya nemi babban bankin Najeriya,CBN ya biya diyyar Miliyan 100 da ‘yan Bindigar da suka sace daliban jami’ar Greenfield dake Kaduna suka nema kamin lokaci ya kure.

 

Malamin yace yana kira ga gwamnati kada ta dauki barazanar da ‘yan Bindigar suka yi da wasa.

 

Malamin ya bayyanawa Punchng cewa, kudin da ‘yan Bindigar ke nema sun yi yawa,kuma kudi ne da idan aka basu ba zasu iya guduwa da su ba.

 

Yace abinda ya kamata a yi shine a basu kudin dan su saki daliban, yace ai mu ba wawaye bane, ta ina zasu iya guduwa da kudin? Yace kamata a dauko kudin daga CBN a basu, daga baya sai a bisu a kwato kudin.

 

Yace yana kokarin ganin an sako daliban amma baya samun goyon bayan Gwanati, yace Boko Haram na kokarin Shiga Lamarin dan dan haka ne ma yake kokarin ganin an jawo ra’ayin ‘yan Bindigar kamin Lokaci ya kure.

 

He said, “ The money they are asking for is too much; if I give you that money, you cannot run away with it. Nobody can run. So, why not give them the money, they release the boys and then we pursue them and get our money back and do what is necessary; it is simple logic.  So, bring the money from the central bank. How can they move that money? We should not be stupid.

 “These people are getting infiltrated; Boko Haram is getting close and they don’t respect the clergy. I need support to get them inoculated against the infiltration of these ideologies, whether Boko Haram or Ansaru, whatever it is. We need to shield them because they are naïve. If there is too much pressure on them, and they see help from Boko Haram, who are richer and have more weapons, it is going to consume everybody.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *