fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Ya kamata ka kama Abba Kyari kamar yanda akawa Sunday Igboho>>Reno Omkri ga Buhari

Hadimin Tsohon Shugaban kasa,  Reno Omkri ya nemi shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kama Abba Kyari kamar yanda yayi yunkurin kama Sunday Igboho cikin gaggawa.

 

Yace sun zuba ido su gani ko za’a nuna musu cewa, wani dan kasa yafi wani muhimmanci.

 

Ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta inda yahi zargin cewa, da Abba Kyari Inyamuri ne da tuni an kamashi.

 

Wasu Rahotanni dai sun hada Abba Kyari da Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi wanda kasar Amurka ta kama bisa zargin damfara. Ya bayyana cewa, ya baiwa Abba Kyari wasu makudan kudade dan kama wani abokin hamayyarsa.

 

Amma Abba kyarin ya musanta wanna  zargi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *