fbpx
Wednesday, June 23
Shadow

Ya kamata mu koyawa Kasar Isra’ila darasi kan kisan da takewa Falasdinawa>>Shugaban kasar Turkey

Shugaban kasar Turkiyya, Racep Tayyip Erdogan ya turawa takwaransa na kasar Rasha, Vladimir Putin cewa ya kamata su koyawa kasar Isra’ila darasi kan kisan da takewa Falasdinawa.

 

Ya bayyana hakane a wata ganawa da suka yi ta wayar tarho, kamar yanda wakilan gwamnatin kasar Turkey suka bayyana.

 

Hakan na zuwane yayin da kazamin fada ke ci gaba da wakana tsakanin Yahudawan Isra’ila da Falasdinawa.

 

Fadan ya samo Asali ne yayin da Kasar Isra’ila ke kokarin tashin Falasdinawa daga wani yanki da ake cewa, Sheikh Jarra dan ginawa mutanen kasarta gidaje, kamar yanda Aljazeera ta ruwaito.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *