fbpx
Saturday, December 4
Shadow

Ya Rasu Bayan Ya Bada Hantar Sa Don Ceto Rayuwar Mahaifiyarsa

Muna yawan jin labarin son da uwa take yi wa ‘ya’yanta, sai dai a wannan lokacin ba son uwa bane, soyayyar da ne ga uwa.

Wani matashin saurayi mai suna Umar Faruk Bajwa, ya tallafi rayuwar mahaifiyarsa, ta hanyar ba ta hantar shi domin ganin ya ceto rayuwarta.

Mahaifiyar ta rayu, amma dan bai rayu ba.

Umar Faruk Bajwa, ya rasu a Sargodha, kasar Pakistan.

Mamacin dalibi ne a jami’a, kuma ya gano cewa mahaifiyarsa tana cikin rashin lafiya, kuma tana bukatar a yi mata dashen hanta.

Umar faruk yayi- yayi, ya ga babu wata hanya da za a samu, sai ya yanke shawarar bayar da hantar shi ga mahaifiyar shi, domin ganin ya ceto rayuwarta.

Mahaifiyar taji dadi sosai matuka, akan irin soyayyar da dan ta yake nuna mata.

 Amma kuma daga karshe ta yi bakin ciki ganin cewa za ta sanya danta cikin halaka.

Da farko mahaifiyar taki amincewa ta karbi hantar dan ta, saboda ba ta so ya shiga cikin matsala, amma dan ya takura ta akan sai ta karba.

Duka an kai su asibiti, aka yi musu aiki, mahaifiyar ta tashi lafiya lau, amma kuma abin bakin ciki shine, dan ya rasu.

Ya bayar da rayuwarshi domin ganin ya ceto rayuwar mahaifiyarshi.

Matashi da shi wanda yake tunanin yadda zai gabatar da rayuwarshi a nan gaba, amma sai ya gano halin da mahaifiyarshi ke ciki, ya manta da komai ya mayar da hankali wajen ceto rayuwarta.

Muna roko Allah ya jikan Umar Faruk Bajwa, ya saka masa da Aljannah Firdaus.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *