fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Yadda ake sarrafa Tumatir wajan gyara fata tare da Sanya Fata sheki

Tumatir yana da matukar al’fanu wajan gyaran fata kasancewar tumatir yana dauke da sinadarai kamar irin su vitamin A, vitamin C, vitamin K da lycopene duka wadanda suke taimakawa wajan kara lafiyar fata da kuma magance wasu cututukan fata kamar irin su, acne, skin cancer da dai sauransu.
Domin samun fata mai sheki a kwana daya, za a iya samun tumatir daya, sai a hada da kofin madara biyu, sannan a shafa a fuska a kwana da shi. A wanke washe gari domin samun sakamako mai ingantarwa.
Hakanan yin amfani da tumatir yana taimakawa wajan magance maikon fuska, A kan markade tumatir da cucumber sai a barshi yayi kankara sai a ringa gogawa a fuskarki kullum.

Yin amfani da tumatir yana taimakwa wajan magance Tabo a jiki.

Yadda ake shine, Za a hada tumatir da zuma sai a shafa a inda tabon yake, sai a barshi yayi tsawan minti 15  sai a wanke. Za ai hakan har sau biyu a sati.

Kai ! Amfanin tumatir bai kare daga nan ba, Ana iya amfani da tumatir domin sanya fata tai haske, Ana samun tumatir sai a markade shi sannan a hada shi da kurkur sai a shafa yayi minti 15 sai a wanke.

Ana samun tumatir sai a yanka shi gida biyu sannan a samu sikari sai a zuba shi akan sa, sannan a ringa gogawa a kowanne sako da lungu na fuska, sannan a barshi tsawan mintuna 15 sannan a wanke da ruwan Dumi hakan na karawa fuska sheki da kyau matuka.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *