fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Yadda Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Rushe Makarantar Ƴan Shi’a Mai Suna ‘Fudiyya’ A Zariya

Rahotanni daga jihar Kaduna sun bayyana cewa; gwamnatin jihar ta rushe wata shahararriyar makarantar ƴan Shi’a Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky dake zariya ranar Alhamis wacce take Babban Dodo Zariya.

A satikan baya de gwamnatin ta bada sanarwar zata rushe gidaje dubu 10 domin kudirin ta bunƙasa kasa da kuma tsara sabon fasali da tsare tsare jihar kamar yanda ta bayyana a kwanakin baya kaɗan.

Rushe gidaje da kasuwanni da sauran gine gine sun zama ruwan dare a jihar Kaduna, ko a baya an rushe kasuwar Bacci, da wasu fitattun wajaje a jihar, wanda hakan yana jefa duban mutane shiga halin ƙaƙanikayi da matsin rayuwa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *