fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Yakamata a duba lafiyar kwakwalwarka – Wike ya gayawa Gwamna Umahi bayan yayi addu’ar Allah ya ba Najeriya wani Shugaba kamar Buhari a 2023

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, yayi wa takwaransa na jihar Ebonyi, David Umahi zazzafar martani, bayan ya yi addu’ar Allah ya ba Najeriya wani shugaban da ke da kyakkyawar zuciya kamar Shugaba Buhari a 2023.

Gwamna Umahi ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da yake zantawa da manema labarai na fadar gwamnati bayan ganawa da shugaban kasa a Aso Villa a Abuja.

Da yake magana a taron masu ruwa da tsaki a Fatakwal a ranar Laraba, 8 ga Satumba, Gwamna Wike ya ce Umahi na bukatar a duba lafiyar kwakwalwarsa, inda ya kara da cewa Shugaban kasar da kansa ya san cewa Allah ba zai ba kasar wani shugaba irin sa ba a 2023.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *