fbpx
Friday, May 14
Shadow

Yan banga sun kama wasu shahararrun masu aikata miyagun laifuka a kasuwar Bayelsa

Wasu jami’an ‘yan banga na jihar sun kame wasu shahararrun masu aikata laifuka guda biyu wadanda suka kware a harkar fashi da makami ga yan kasuwa da masu siye a Kasuwar Tombia da ke karamar hukumar Yenagoa ta Jihar Bayelsa.

Wadanda ake zargin sun hada da Kingsley Maxwell mai shekaru 20, da James Ebi, 23, an kamasu ne a ranar Talata, 27 ga Afrilu, jim kadan bayan sun yi wa wata Gold Ebi fashin, yayin da take sayen kayan abinci a kasuwar Tombia.

‘Yan banga sun kama wasu shahararrun masu aikata miyagun laifuka a kasuwar Bayelsa.

A cewar yarinyar, tana cikin kasuwar ne lokacin da ‘yan fashin biyu suka yi mata fyaden suka kwace jakarta.

“Nan da nan tayi ihun neman agaji wanda hakan yasa aka sanar da jami’an ‘yan banga na jihar Bayelsa wadanda ke kusa da kasuwar a lokacin, kuma suka bi su suka cafke su.

‘Yan kasuwa da masu tafiya a kafa a cikin kasuwar sun tabbatar da cewa wadanda ake zargin sun kasance suna addabar kasuwannin a kullum, a kowace  rana.

An mika mutanen biyu ga jami’an tsaro na kodin na ‘yan sanda mallakar jihar mai suna Operation Dou Akpo

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *