fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Yan bindiga a shirye suke su ajiye makamai, idan akayi masu musu afuwa – Sheik Gumi

Babban Malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Ahmad Gumi, ya sake jaddada kiran da ya yi na a yi wa ‘yan fashi da makiyaya afuwa.

Gumi ya ce ‘yan bindiga a shirye suke su ajiye makamansu, don haka ya kamata gwamnatin tarayya ta yi musu afuwa.

Ya bayyana cewa yin afuwa ga ‘yan bindigan zai kawo karshen zubar da jini da tashin hankali a Arewa.

Malamin ya yi jawabi ne a wajen karbar kashi na uku na dalibai a cikin shirin tallafawa marayu na kiwon lafiya da ilimi kyauta wanda gidauniyar Kawo Islamic Foundation ta shirya a Kaduna.

Ya bukaci gwamnatin tarayya da ta ilmantar da ‘yan fashi da basu jarin kudade bayan ta yi musu afuwa.

A cewar Gumi: “Idan har akwai abin da zai hana zubar da jini, gara kamar yadda ya faru da tsagerun Neja-Delta, suna zubar da jini suna lalata bututun mai, amma sai suka yi shirin jefar da makamansu tare da yi musu afuwa, wanda zai kula da su, ina ganin irin hakan zai iya shafar makiyaya.

“Mun gamu da su kuma a shirye suke su ajiye makamansu, amma idan suka ajiye makamansu idan ba ku ilimantar da su ba, ba ku ba su kudaden da za su kula da su ba, za su koma yadda suke a da.

“Har yanzu, muna kira da a yi afuwa tare da dakatar da duk wani tashin hankali saboda mun san yadda za mu magance shi cikin lumana.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *