fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

‘Yan Bindiga da ake zargin ‘yan IPOB ne sun kaiwa Ofishin DSS hari, DSS din sun ce daga yanzu ba zasu sake lamuntar irin wannan hare-haren ba

Bayan Ofishin Hukumar zabe me zaman kanta, INEC da ‘yan Bindiga suka kaiwa hari a jihar Akwa-Ibom,  sun kuma kaiwa Ofishin DSS hari.

 

Baturen zabe na jihar, Mike Igini ya bayyana haka inda yace ofishin DSS din na kusa da Ofis dinsu, yace an kai masa hari amma ba’a konashi ba.

 

Hakanan a wani lamari me kama da wannan, hukumar ta DSS ta gargadi masu yiwa hadi  kan Najeriya barazana su kuka da kansu su daina.

 

Kakakin hukumar, Peter Afunanya ya bayyana cewa daga yanzu ba zasu sake aminta da yunkurin wasu kungiyoyi na jefa kasar cikin rikici ba, yace sun hada kai da sauran jami’an tsaro dan maganin matsalar.

“While the Service reaffirms its unambiguous support to an indivisible, indissoluble and united Nigerian State in accordance with the provisions of the Constitution, it will no longer tolerate deliberate machinations by subversive and hostile groups whose agenda is to throw the country into anarchy so as to serve the interests of their sponsors.

“Consequently, the Servcie is assiduously working with other security and law enforcement agencies to ensure the maintenance of peace and internal security of the country.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *