fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Yan bindiga sun kai hari a jihar Katsina, inda suka sace yaran hakimin wani kauye

Wasu ‘yan bindiga a ranar Litinin sun kai hari kauyen Sabuwar Kasa, da ke karamar hukumar Kafur a jihar Katsina inda suka yi garkuwa da yara hudu na hakimin kauyen, Alhaji Hamza Umar.

A yammacin Litinin, mazauna yankin sun tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun kai hari kauyen ranar Litinin, inda suka kara da cewa ba ya nan a lokacin da lamarin ya faru.

Hakimin kauyen kuma shine shugaban ayyuka a karamar hukumar Funtua.

Ba za a iya tuntubar Umar don jin ta bakinsa ba a ranar Litinin, duk da cewa dangi sun ce baya cikin kauyen lokacin harin.

Har yanzu ana jiran martanin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *