fbpx
Saturday, June 19
Shadow

Yan bindiga sun kai hari a jihar Neja, inda suka kwashe kayan shagunan, tare da saci shanu 250

Yan bindiga sun kai hari garin Warari da ke karamar hukumar Rijau a jihar Neja.

Daruruwan mutane sun tsere daga gidajensu yayin da ‘yan bindigar suka afkawa kauyen da babura 50, dauke da mutane 3 kowanne.

Wadanda suka yi sa’a sun bar gidajensu kimanin awa daya kafin ‘yan fashin su iso.

“Mun samu labarin harin ne daga wasu mazauna kauyukan wasu garuruwan da suka afkawa kafin su zo Warari”, in ji wani mutumin yankin.

Wadanda suka tsere daga harin sun koma garin Rijau, a cewar PRNigeria.

Akalla shaguna 10 ne barayin suka yi wa fashi da makami. Wannan shi ne hari na shida a cikin watanni uku da suka gabata.

Bayan harin na Warari, ‘yan ta’addan sun koma kauyukan Argida, Gero da Magaman Daji, inda suka yi awon gaba da shanu sama da 250.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *