fbpx
Saturday, December 4
Shadow

Yan bindiga sun kai hari a jihar Zamfara, inda suka kashe mutane 7 tare da sace dabbobi 1,500

Yan bindiga sun kai farmaki kauyen Yanbuki da ke karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara inda suka kashe mutane bakwai tare da sace shanu da tumaki 1,5000.

Wani dan kauyen mai suna Garba Musa ya shaida wa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyen ne a daren ranar Talata, inda suka yi ta harbi ba kakkautawa.

Musa ya ce, “Nan da nan suka isa, sai suka bude wuta ga duk wanda suka gani. Kowa ya gudu don kare kansa.

“Daga baya sun koma gida gida, suna neman kayan abinci da dabbobi sannan kuma sun fasa shaguna da dama.

“Sun kuma yi awon gaba da dabbobi sama da 1,500 kamar shanu, tumaki da awaki.”

Ya kara da cewa bayan ‘yan bindigar sun bar kauyen ne mazauna garin suka fito daga maboya, inda suka gano cewa an harbe mutane bakwai har lahira, yayin da wasu kuma suka samu raunuka.

“Mun binne mutanen bakwai, amma adadin wadanda suka mutu zai iya zarce haka saboda wasu mutane sun gudu zuwa daji kuma har yanzu ba a gansu ba.”

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu, ya tabbatar da faruwar harin.

Ya kara da cewa, “Tuni kwamishinan ‘yan sandan ya baza jami’an ‘yan sanda isassu a yankin domin a samu zaman lafiya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *