fbpx
Friday, May 14
Shadow

Yan Bindiga Sun Kai Hari A Sansanin Sojoji,Inda Suka Kashe Mutum Daya a jihar Nijar

Yan bindiga sun kai hari kan sansanin sojoji a garin Zazzaga, karamar hukumar Munya da ke jihar Neja.
An kashe farar hula daya mai suna Jacob Auta sannan an sace motar sojoji a yayin harin wanda aka kai da misalin karfe 4:00 na yamma a ranar Laraba.
Shaidun gani da ido sun ce ‘yan bindigar wadanda yawansu ya kai dari, sun zo ne a kan babura yayin da suka afkawa yankin, suna harbi a kan lokaci-lokaci a sansanin.
An kone sansanin tare da kuma kona wasu motocin sojoji yayin harin.
Kodayake sojojin sun samu nasarar dakile harin, amma ‘yan ta’addan sun kona dukiyoyinsu.
Wani shugaban matasa a yankin, Usman Babangida ya fadawa gidan talabijin na Channels cewa an yi musayar wuta tsakanin sojoji da ‘yan bindigar wanda ya dauki sama da awa daya.
An ce an kashe wasu daga cikin ‘yan fashin kuma maharan sun tafi da gawarwakinsu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *