fbpx
Saturday, December 4
Shadow

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari A Borno Bayan Ziyarar Da Shugaba Buhari Ya Kai Jihar

Wasu mahara wa ‘yan da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne, sun kai hari a unguwar Jiddari Polo, da ke cikin babban birnin Maiduguri. 

Wannan sabon harin, ya zo dab da awanni biyu, bayan ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buharin ya kai a birnin Maiduguri, inda mayakan suka kai farmaki unguwar a daidai lokacin sallar magariba.
Kamar yadda wakilin leadership, ya tattauna da jama’a da dama a unguwar, daga ciki akwai Malam Shettima Umar wanda ya bayyana cewa, ”yanzu haka sai karar harbe-harben manyan bindigogi, jama’a kuma suna ta gudu  kowa ta kansa yake yi”.
Gaskiya al’amari ne mai daure kai, ganin cewa harin yazo yan awanni kadan, da ziyarar shugaban kasa Muhammadu Buhari, yayi a nan birnin Maiduguri. 
Wannan wane irin abu ne haka, wane laifi muka yi ne haka da har bamu cancanta mu samu kwanciyar hankali ba.
Wasu bayanan kuma sun tabbatar da cewa, kararar bindigogin tana dan lafawa, sannan kuma jami’an tsaro na ci gaba da kai dauki a unguwar.
Allah ya tsare mu.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *