fbpx
Saturday, October 16
Shadow

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari A Malumfashi Sun Kashe Malamin Jami’a

A daren jiya Litinin ne, ‘yan bindiga dauke da manyan bindiogi suka dira karamar hukumar Malumfashi, inda suka fara harbe-harbe har suka kashe wani Malamin Makarantar share fagen shiga jami’a ta Ahmadu Bello dake Funtua, Malam Umar Faruq Isa Funtua.

Wani mazaunin garin Malumfashi, wanda bai so a ambaci sunansa, ya shaidawa RARIYA ta waya cewa ‘yan bindigar sun kai hari ne gidan wani shahararren dan kasuwa dake zaune a unguwar Kwandala a garin na Malumfashi.
Ya ce “a kokarin ‘yan bindigar na ganin sun samu sun shiga gidan ne, suka fara harbe-harbe ba kyafkyaftawa, kuma har ya yi sanadiyyar kashe Malam Umar Faruq har lahira”.
A wani labarin kuma, ‘yan bindigar, a daren shekaran jiya Lahadi, sun shiga garin Tsauri da ke karamar hukumar Kurfi inda suka kashe wani matashi mai suna Yasir Usman Tsauri.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *