fbpx
Monday, May 10
Shadow

Yan bindiga sun kai hari sansanin sojoji a jihar Neja, sun bankawa motoci wuta

Wasu yan bindinga da adadin su ya kai 60 dauke da muggan makamai sun kai hari a wani sansanin sojoji da ke garin Zazzaga na karamar hukumar Munya ta jihar Neja da sanyin safiyar ranar Laraba 21 ga Afrilu.

Babu wani soja da ya rasa ransa a wannan sabon harin wanda ya zo kusan makonni uku bayan da ‘yan ta’addan suka kai hari kan sansanin jami’an tsaro na hadin gwiwa da ke Allawa da Basa a karamar hukumar Shiroro da ke jihar, inda suka kashe sojoji biyar da wani Dan Sanda.

An bayyana cewa yan bindingar sun afkawa garin da misalin karfe 4:00 na safe kuma sun raba kansu zuwa kungiyoyi uku. Yayin da wata kungiya tabi hanya kai tsaye zuwa sansanin sojoji da ke karamar makarantar sakandare mai nisan kimanin mita 500 daga garin inda suka yi artabu da sojoji, rukuni na biyu sun yi kwanton bauna a kan babbar hanyar da ke zuwa garin.

Kungiya ta uku suka dau hanya zuwa ga al’umma don hana duk wani yunkuri na ‘yan banga garin ko matasa.

An ruwaito cewa wata majiya ta ce bayan kimanin sa’o’i biyu suna musayar wuta daga 4:00 na safe zuwa 6:00 na safe, alburusan sojoji suka kare, sai suka gudu. Bayan sojojin sun sun gudu sai yan bindingar suka kutsa sansanin, suka bankawa motocin sojoji wuta sannan suka tafi da wani yayin da kuma suka kona rumbunan abincin da ke sansanin.

Wani sojan da aka bayyana a matsayin RSM na sansanin an bayar da rahoton cewa ya ɓace; har yanzu ba a san inda yake ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *