fbpx
Monday, September 27
Shadow

‘Yan Bindiga sun kai hari sansanin Sojoji sun kashe 12 a Zamfara

‘Yan Bindiga sun tashi wani sansanin Sojoji a Zamfara a wani hari da suka kai.

 

Wannan ya kawo koma baya a kokarin kakkabesu da ake yi a jihar.  Sojoji 12 ne suka rasa rayukansu a harin.

 

Lamarin ya farune a Mutumji dake Dansandau me nisan Kilometres 80 da ga babban birnin jijar, Gusau.

 

Akwai Sojojin sama 9 dana kasa 1 da kuma ‘yansanda 2 da aka kashe a harin.

 

An kai gawarwakin sojojin da aka kashe asibitin Yeriman Bakura sannan kuma an kai guda 3 da suka jikka inda ake basu kulawar data kamata.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *