fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Yan bindiga sun kaiwa kauyukan jihar Filato hari, sun kashe mutane hudu, tare da kona gidaje da dama

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun sake kaiwa wasu al’ummomi a karamar hukumar Bassa ta jihar Filato hari, inda suka kashe mutane hudu yayin da aka kona gidaje da dama.

An bayyana cewa harin, wanda kuma yayi sanadiyyar raunata mutane da dama, ya faru ne yayin da mutanen ke bacci a daren Asabar.

Shugaban kungiyar ci gaban Irigwe ta kasa, Ezekiel Bini ya tabbatar wa da manema labarai harin a Jos ranar Lahadi.

Bini ya ce, “Makiyaya sun sake kaiwa mutanen mu hari a daren jiya. Wannan harin musamman ya fi yin barna.

“Maharan sun kona gidaje daga Kauyen Zamuna da na kusa da Jebbu Miango.

“Sun kara lalata gonakinmu ta hanyar yankar albarkatun gona tare da kona gidaje da dama. An tabbatar da mutuwar mutane hudu da raunata da dama. ”

An tura jami’an tsaro zuwa wurin da abin ya faru.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *