fbpx
Monday, November 29
Shadow

‘Yan bindiga sun kakkabo jirgin ‘yansanda bayan kashe ‘yan bindiga 250

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sanar da cewar wasu ‘yan bindiga a yankin Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna sun harbo mata jirgin sama mai saukar ungulu bayan da ya kai musu hari inda ya hallaka sama da ‘yan bindiga 250 daga cikin su.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Mai Magana da yawun rundunar Frank Mba ya ce jirgin wanda ke cikin masu kai hare hare kan ‘yan bindigar da suka addabi Jihar ya gamu da hari daga ‘yan bindigar da ke amfani da na’uarar kakkabo jirage da kuma manyan bindigo abinda ya sa matuka jirgin suka yi amfani da kwarewar su wajen sauka a tashar sojin sama da ke Kaduna.

A cewar mai magana da yawun rundunar ‘yansandan ta Kaduna yanzu haka an kwashe matukan jirgin domin kula da lafiyar su sakamakon raunin da suka samu, yayin da aka dauki jirgin zuwa Abuja.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *