fbpx
Friday, May 14
Shadow

Yan bindiga sun kashe babban limamin gari tare da wani mutum a jihar Zamfara

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin‘ yan fashi ne, a ranar Litinin, sun kai wani mummunan hari a kan al’ummar Kwangwami da ke cikin Karamar Hukumar Zurmi ta Jihar Zamfara, inda suka kashe Babban Limamin, Alhaji Liman Auwalu na masallacin Juma’a na Kwangwami da kuma wani dan gari daya.
A cewar mazauna kauyen, ‘yan fashin sun lalata gonaki da dama tare da yin awon gaba da shanu da sauran kaddarorin mazauna kauyen.
A cewar wani shaidar gani da ido, wani mai suna Ibrahim Kwangwami, ‘yan fashin sun mamaye yankin da yawansu a kan babura inda suka fara harbi lokaci-lokaci.
Jaridar DAILY POST ta tattaro cewa harsashi ya sami babban limamin, Alhaji Liman Auwalu yayin da dayan wanda aka sani da Hamisu Bako aka harbe shi a gonarsa.
Lokacin da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO), SP Mohammed Shehu ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya nuna cewa an tura jami’an‘ yan sanda dauke da muggan makamai don tseratar da yankin, yana mai cewa ana kokarin kama wadanda suka aikata aika-aikar.
A cewar Shehu, al’amura sun koma yadda suke a yanzu, yana mai jaddada cewa kowa yana yin abin da ya dace ba tare da fargaba ba kasancewar an tura ‘yan sanda bakin aiki.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *