fbpx
Thursday, May 6
Shadow

Yan bindiga sun kashe jami’in kwastam tare da raunata wani a Jigawa

Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani jami’in kwastam tare da jikkata wani a yayin da suke sintiri a kauyen Kyarama da ke karamar Hukumar Ringim a Jihar Jigawa.
Daily post ta labarta cewa lamarin ya faru ne lokacin da wasu ‘yan daba suka yi shigar burtu a matsayin masu ba da rahoto, suka kira jami’an kwastam din suka sanar da su cewa akwai wata mota da aka yi fasa kwaurin shinkafa da ita kan hanya.
An ce ‘yan bindigar sun bude wuta ne kan wadanda abin ya shafa bayan sun isa wurin.
Kakakin rundunar yan sanda, SP Abdu Jinjiri ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar DAILY POST.
Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da misalin karfe 4:30 na safe. yayin da jami’an kwastam ke sintiri.
Jinjiri ya bayyana cewa wasu ‘yan daba wadanda ba a san su ba ne suka far wa jami’an a kan kauyen Kyarama da ke karamar hukumar Ringim.
Ya ce an kashe daya daga cikin jami’an, yayin da dayan ya samu mummunar rauni sakamakon harbin bindiga.
Ya ce ‘yan bindigar sun kuma yi awon gaba da kananan bindigoginsu biyu.
Ya ce, ana kokarin gano wadanda suka aikata laifin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *