fbpx
Monday, May 10
Shadow

‘Yan Bindiga sun kashe Kwamishina a jihar Kogi

‘Yan Bindiga da ba’a kai ga tantancesu ba, sun kashe kwamishinan jihar Kogi a daren jiya, Asabar.

 

Solomon Adebayo, Kwamishinan Fansho ne ga Gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello. Yana kuma tafiya zuwa Kabba ne daga jihar Ilorin yayin da lamarin ya faru dashi.

 

‘Yan Bindigar sun budewa motarsa wuta inda suka kasheshi nan take. Sun kuma jikkata direbansa sosai, kamar yanda kakakin ‘yansandan jihar, William Ayah ya bayyana.

 

Yace an tafi da direban Asibiti, kuma zasu fara bincike dan gano wanda suka yi wannan aika-aika. Yace babu tabbas ko maharan sun tafi da wasu kayan Amfanin Kwamishinan.

Peoplesgazette

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *