fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

‘Yan Bindiga sun kashe Manoma 41 da dansanda a jihar Zamfara

Lamarin ya farune a Tofa da Samawa dake karamar hukumar Bugudu a jihar.

 

Wani mazaunin yankin yace maharan sun je ne yayin da manoman ke shuka a gonakinsu. Malam Balarabe yace sun fara harbin kan mai uwa da wabi inda suka kashe da yawa.

 

Ya kara da cewa sun kuma tare hanya inda suka rika kashe manoman dake kan hanyar komawa gidajensu, yace basu dauki komai ba amma sun kashe manoma 41.

 

Kakakin ‘yansandan jihar, Muhammad Shehu ya bayyana cewa, ba’a sanar dasu faruwar lamarin Tofa ba saida ‘yan Bindiga suka gama abinda suke.

 

Yace amma da suke kan hanyar zuwa Samawa, ‘yansanda sun taresu inda suka kashe da yawa, wasu suka jikkata. Ya kara da cewa, Dansanda daya ya mutu.

“However, as the bandits left Tofa on their way to Samawa village for similar attack, the Police Tactical operatives stationed at Samawa village were quickly alerted where they mobilised and engaged the assailants in a serious gun battle that lasted for hours.

“As a result of the encounter, unspecified number of bandits was fatally injured (killed), while others escaped with possible gunshot wounds. No loss of life from the community in Samawa, but regrettably, a police operative paid the supreme price during the gun battle with the bandits,” Shehu said.

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *