fbpx
Saturday, December 4
Shadow

Yan bindiga sun kashe matan aure da wasu, sun kona gidaje a Taraba

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyukan Binnari da Jab Jab da ke karamar hukumar Karim Lamido a jihar Taraba da misalin karfe 4 na safiyar Laraba 10 ga watan Nuwamba.

Aminiya ta ruwaito cewa akalla mutane 15 ne suka mutu, ciki har da matan aure uku a yayin harin. An ce mutanen kauyen sun yi yunkurin fafatawa amma ‘yan bindigar da aka ce sun haura 50 sun yi galaba a kansu.

An yi zargin cewa ‘yan fashin sun kai hari kauyukan biyu ne a matsayin ramuwar gayya da kashe wasu masu garkuwa da mutane da ‘yan banga suka yi a yankin makonnin da suka gabata. An kashe ‘yan bindiga 7 a yayin arangamar kuma ‘yan bindigar da suka tsira daga harin sun tsere da gawarwakin ‘yan kungiyarsu.

Yan bindigar da suka kai harin ramuwar gayya, sun kashe mutane da dama tare da kona gidaje. Mazauna garin sun koka da rashin jami’an tsaro.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *