fbpx
Saturday, June 19
Shadow

‘Yan Bindiga sun kashe matansu dake shirin Tona musu Asiri: Hotunan yanda suka kai jami’an tsaro kabarin da suka binnesu

Wasu ‘yan Bindiga 2 da aka kama a jihar Osun wanda sun fito ne daga jihar Benue sun bayyana yanda suka kashe matansu.

 

‘Yan Bindigar na cikin wasu gungun ‘yan bindiga ne da suka addabi al’umma da aikata miyagun Laifuka.

 

Bayan kamasu, sun kai ‘yansanda wani kabari a Katsina Ala ta jihar Benue inda anan ne suka binne matansu 2 da kuma wasu da suka yi garkuwa dasu.

Masu laifin, Aondoaseer Teseer da Okashima David duk sun amsa laifin kashe matansu. A kabarin da suka kai jami’an tsaro, an gano mata 3 da maza 3.

 

Sunce 2 daga cikin matan matansu ne da suka kashe da kansu.

 

Kakakin ‘yansandan jihar, DSP Catherine Anene ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace tana jiran jawabin yanda lamarin ya kasance daga wajan abokan aikinta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *