fbpx
Sunday, September 26
Shadow

Yan bindiga sun kashe Mopol,’ yan banga biyar, sun yi garkuwa da mutane 23 a Kaduna

‘Yan bindiga sun kashe wani dan sandan mopol tare da yin garkuwa da mutane 23 yayin harin da suka kai Ungwan Sauri da Adnayita a yankin Juji, dukkansu a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Sun kuma kashe ‘yan banga biyar a wani harin kwanton bauna da aka kai musu a Udawa a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari yayin da wani dan kungiyar ya tsira daga harin da raunin harsashi.

A Ungwan Sauri da Adnayita da ke Juji, an samu labarin cewa ‘yan bindigar sun mamaye yankin ne da sanyin safiyar Laraba, inda suka rika harbe -harbe tare da kashe dan sandan.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya tabbatar da harin, ya kara da cewa tuni aka tura jami’an rundunar zuwa yankunan.

Sai dai kakakin ‘yan sandan bai iya ba da cikakken bayani kan adadin mutanen da maharan suka tafi da su ba.

Amma wata majiya, wani dan banga ya shaida wa jaridar The Nation cikin aminci, cewa ‘yan bangan sun sace akalla mutane 23.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *