fbpx
Saturday, June 19
Shadow

‘Yan Bindiga sun kashe mutane 5 a Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa, ‘yan Bindiga sun kashe mutane 5 a kananan hukumomin Chikun da Igabi.

 

Kwamishinan harkokin cikin gida na jihar, Mr. Samuel Aruwan ne ya bayyana haka ga manema labarai.

 

Yace mutane 2 ne aka kashe a karamar hukumar Chikun da kona gidaje 2 da wajan Ibada.

 

Yace an kuma kashe mutane 3 a Lambar Zango dake kan hanyar Kaduna zuwa Zaria. A karamar hukumar Igabi dake jihar.

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *