fbpx
Friday, January 21
Shadow

‘Yan Bindiga sun kashe mutane 52 a wani harin da suka kai jihohin Naija da Filato

A wasu hare-haren da ‘yan Bindiga suka kai a jihihin Naija da Filato sun kashe mutane 52.

 

Mutane 18 ne aka kashe a yankin Ncha na karamar hukumar Bassa ta jihar Filato sannan kuma a jihar Naija, mutane 34 ne aka kashe a wasu hare-hare daban-daban.

 

Harin jihar Naija na ramuwar gayya ne da ‘yan Bindigar suka kai kan ‘yan banga da mafarauta bayan kisan da suka musu a baya.

 

Hare-haren sun farune a Nakuna da Wurukuci inda kuma ‘yan Bindigar suka kona gidaje akalla 200.

 

A jihar ta Naija, Shaidu sun ce sai an daure hannun mutum ta baya sannan a dirka masa harsashi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *