fbpx
Friday, April 23
Shadow

Yan bindiga sun kashe mutane 8 tare da jikkata 4 yayin da suka bude wuta kan matafiya a Jihar Kaduna

Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane 8 sannan hudu suka jikkata a wasu hare-hare daban-daban a kananan hukumomin Kajuru da Kachia na jihar Kaduna.

Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Talata 6 ga Afrilu, ya ce ’yan bindigar sun tare hanyar Kaduna zuwa Kachia da ke kusa da kauyen Kadanye a karamar Hukumar Kajuru, sannan suka bude wuta a kan motar bas, da kuma babbar mota dauke da itacen girki.

An kashe mutane biyar a harin da aka kai da sanyin safiyar Talata, 6 ga Afrilu.

Mutane uku sun ji rauni kuma yanzu haka suna karbar magani a asibiti.

Hakazalika, wasu ‘yan fashi da makami sun tare hanyar Kaduna zuwa Kachia a layin Doka da ke karamar hukumar Kajuru, inda suka kashe direban.

Bugu da kari, a karamar hukumar Kachia, ‘yan bindiga sun mamaye kauyen Inlowo, inda a nan ma suka kashe wani Ibrahim Alhaji Haruna, kafin su kwashe shanu 180.

A kauyen Akilbu da ke karamar hukumar Kachia, wasu ‘yan bindiga dauke da bindiga sun buda wuta inda suka jikkata mutum biyu, amma bayan an kai su Asibiti dayan ya mutu.

Kwamishinan ya ce gwamna Nasir El-Rufai yayi Allah wadai da wannan iftila’in, kuma ya aike da ta’aziya ga iyalan mamatan, yayin da ya yi addu’ar samun juriya. Ya kuma yiwa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *