fbpx
Friday, April 23
Shadow

Yan Bindiga sun kashe mutane 9 a sabon harin da suka kai Kaduna

.’Yan Bindiga sun kai hari a jihar Kaduna sun kai wani mummunan hari a kananan hukumomin Giwa da Birnin gwari wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane 9.

 

Kwamishinan harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ne ya bayyana haka ranar Alhamis, saidai be fadi lokacin da abinbya faru ba.

 

Yace ‘yan Bindigar sun kai hari kan titin Dogon Dawa zuwa Kuyello inda suka kashe mutane 6. Sunayen wadanda aka kashe sune, Nura Rufai, Sanusi Gajere, Yakubu Labbo, Usman Dangiwa, Alhaji Abdulhamid, Janaidu Tsalhatu.

 

Yace a anguwan Maje kuma sun kashe mutane 2, Haruna Dotu da Hamisu Muhammad, sai kuma Nasiru Rufai da suka kashe a kauyen Kwama dake karamar hukumar Giwa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *