fbpx
Saturday, April 17
Shadow

Yan Bindiga sun kashe mutane biyar a jihar Kaduna

Wani mummunan lamari ya faru a ranar Lahadi a karamar hukumar Chikun da ke jihar Kaduna yayin da wasu ‘yan bindiga suka far wa kauyen Katarma da ke cikin karamar hukumar, inda suka kashe mutane biyar tare da jikkata wani mutum guda.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan, ya ce ’yan bindigar sun far wa al’ummar ne da sanyin safiyar yau kuma suka fara harbin kan mai uwa da wabi wanda ya yi sanadin mutuwar mutanen biyar.
A wani lamarin, sojojin na ‘Operation Safe Haven’ sun ba da rahoton wani rikici tsakanin wasu matasa a ƙauyen Atuku na ƙaramar hukumar Jema’a, yayin da wani Afiniki Thomas ya samu mummunan rauni a goshinsa bayan da wasu matasa biyu suka far masa.
Daya daga cikin maharan, Sani Safiyanu an kama shi don yin bincike yayin da aka garzaya da wanda yaji rauni zuwa asibiti don kulawa.
Bugu da kari, sojojin na ‘Operation Safe Haven’ yayin da suke aikin sintiri sun gano gawar wani Paul Simon, da ke zaune a kauyen Yagbak da ke karamar hukumar Zangon Kataf. An bayyana marigayin ya bata a ranar 24 ga Maris.
A halin yanzu, Gwamna Nasir El-Rufai ya nuna bakin ciki kan abubuwan da suka faru.
Gwamnan ya aike da ta’aziyya ga dangin mamatan yayin da yake yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa.
Ya kuma nemi hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike kan rikicin a kauyen Atulu da ke karamar hukumar Jema’a.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *